Sojoji Sun Yi Arangama Da ‘Yan Boko Haram A Damboa
Kakakin shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya a Maiduguri, Kanar Muhammad Dole, ya ce wasu sojoji dake aikin sintiri sun wargaza wani yunkurin da mayakan Boko Haram suka yin a kai farmaki kan garin Damboa da wani barikin soja dake can da asubahin yau, suka yi barna mai yawa ma tsageran.
A cikin wata sanarwar da ya aikewa da ‘yan jarida ta hanyar Imel, Kanar Dole ya ce, “an kasha ‘yan ta’addar Boko Haram su 38 a wannan fadan, wasu kuma sun gudu da raunuka dabam-dabam a jikinsu.” Ya kara da cewa an lalata motocinsu guda uku.
Kanar Dole yace an gano nakiyoyi da bama-bamai a cikin mota guda. Haka kuma an samu muggan makamai, ciki har da manyan bindigogi na mashin-gan.
An kasha soja guda daya, yayin da wasu guda biyu suka ji rauni a wannan artabu da aka yi.
Sanarwar ta Kanar Dole, ta kara da cewa, “Sojojin kasa da jiragen saman yaki sun a farautar ‘yan ta’addar da suka gudu a nan yankin Damboa da kauyukan da suke kewaye da nan.”
Garin Damboa dai yana da tazarar kusan kilomita 90 a kudu maso yamma da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A watan Mayun shekarar da ta shige ne shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa domin murkushe kungiyar Boko Haram da kuma kawo karshen tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane.